EFCC ta ƙulla yarjejeniya da Hukumar abinci ta duniya WFP

Wasu 'yan gudun hijra ke layin karbar abinci

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

EFCC, ta ce za ta tabbatar abincin da Hukumar abinci ta Duniya -WFP. ta tanadar wa 'yan gudun hijira ya kai garesu

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati watau EFCC, ta sanya hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tare da Hukumar abinci ta Duniya -WFP.

Karkashin yarjejeniyar, EFCC ta za ta tabbatar da cewar dukkanin wasu kayan agaji da Hukumar abinci ta duniya ta bayar, sun kai ga wadanda za su amfana da shi, ba tare da wata barazana ta cin hanci ba.

Shugaban riko na Hukumar ta EFCC , Ibrahim Magu da ya sanya hannu a madadin Hukumar EFCCn, ya ce sabon kawancen zai taimaka matuka, wajen warware matsalolin mutanen da suka rasa muhallansu, musamman a sashen arewa maso gabashin Najeriya.

Ibrahim Magu ya ce, "Muna tabbatar maku cewa zamu bi ku duk wani lungu, kuma loko-loko a jihohin arewa maso gabashin kasar, kamar su Yobe da Adamawa, duk dai inda kuke bukatar mu mayar da hankali, idan ma babu jami'an mu a wajen, zamu mu tura su domin su bayar da gudunmuwa wajen ayyukan ku" Ya kuma kara da cewa,

"Zamu tabbatar kayayykin sun kai ga masu bukatat ba tare da barzanara cin hanci ba."

Haka nan shima Daraktan sa-ido da bincike na Hukumar abincin ta duniya WFP, Bernadin Assiene, ya ce, sanya hannu kan yarjejeniyar, wani tabbaci ne cewar Hukumar EFCC ce muhimmiyar kawar taimakawa Hukumar abincin ta duniya, wajen ganin taimakonta ya kai ga wadanda aka nufa da shi ba tare da zamba da kuma muna - muna ba.