Mutane 20 sun mutu a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

Wasu mata a yayin zanga-zangar DRC

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun ce shugaba Kabila na mulki ne ba bisa tsarin doka ba

Majaalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da 20 aka kashe a zanga- zangar da aka yi a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

Jamian tsaro sun harba harsasai kan masu zanga zangar a Kinshasa babban birnin kasar,inda mutane suka toshe hanyoyi tare kuma da kone tayoyi.

An kuma ji karar harbe-harben bindiga a garin Lubumbashi, inda aka kashe jami'an 'yan sanda akalla 2

Masu zanga-zangar sun bukaci shugaba Joseph Kabila da ya sauka bayan da wa'adinsa mulkin sa ya zo karshe a jiya Litinin.

A yanzu haka Mista Kabila ya kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta jangoranci kasar har sai bayan an gudanar da zabe a shekarar 2018.

Sabon Firayi Ministan kasar Samy Badibanga, ya ce gwamnatin za ta tabbatar da tsaro a kasar.