Nigeria:Takaddama a kan Magu da EFCC

Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban EFCC

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban EFCC

A Najeriya, ana ci gaba da cece-ku-ce dangane da gazawar majalisar dattawan kasar wajen tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin kasar zagon-kasa, wato EFCC.

Wani batun da ke jan hankalin jama`a shi ne yadda hukumar tsaron farin-kaya ta gabatar da wasu rahotanni masu karo da juna a kan Ibrahim Magun, rahotannin da majalisar dattawan ta dogara da su wajen jinkirta maganar tabbatarwar.

'Yan Najeriya da dama dai sun cika da al`ajabi ne ganin yadda Hukumar SSS ta yi baki-biyu wajen yin rahoto a kan mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, wadanda aka mika wa majalisar dattawan Najeriyar, inda guda ke cewa Magun ya cika mutumin kirki da zai dace da shugabancin hukumar EFCC, yayin da daya rahoton kuma ke cewa Ibrahim Magu na da laifi.

Babban abin da ya fi daure kai shi ne, mutum daya ne ya rattaba hannu a kan dukkan rahotannin biyu, kuma a rana daya!

Duk da cewa har yanzu hukumar SSS ba ta shaida wa duniya yadda aka yi ta zama bakin-ganga ba, masu lura da al`amura na zargin cewa cin karo da rahotannin hukumar SSS din suka yi alama ce ta rashin iya aiki ko kuma son zuciya.