Za mu magance rikicin Kudancin Kaduna —El-Rufai

Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai
Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai

A Nigeria, gwamnatin jahar Kaduna ta sha alwashin magance matsalolin tsaron da ake fama da su a kudancin jahar.

Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai shi ne ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai tare da wasu jami'an gwamnatin jahar zuwa garin Kafanchan karamar hukumar Jama'a inda aka tafka rikici a ranar litinin din da ta gabata.

Gwamnatin jahar ta zargi wasu 'yan siyasar yankin da ingiza zanga-zangar da ta haddasa rikicin da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Wasu 'yan yankin kudancin jihar dai sun gudanar da karin zanga-zanga a yayin ziyarar da gwamnan ya kai duk da dokar hana fitar da aka sanya a garin na Kafanchan.