Kashi 46 cikin 100 na 'yan Afrika na fama da hawan jini

Masana sun ce hawan jini cuta ce dake hallaka da Adam a boye

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Masana sun ce hawan jini cuta ce dake hallaka da Adam a boye

Wani bincike da hukumar lafiya ta duniya ta gudanar ya gano cewa kimanin kashi arba'in da shidda cikin dari na 'yan Afrika na fama da hawan jini, kuma wannan adadi shi ne mafi girma a duniya.

Binciken ya danganta hakan da karuwar da ake samu ta mutane dake rungumar yanayin rayuwa wadda ke illa ga lafiyar jama'a.

Sai dai wasu masana kiwon lafiya a kasashen Afrika sun ce basu yi mamakin wannan sakamakon bincike ba.

Motsa jiki dai yana cikin abubuwan da likitoci ke cewa suna taimakawa wajen shawo kan matsalolin irin su hawan jinin, da ciwon zuciya, da ciwon suga da dai sauransu.