Jammeh ya yi tir da ECOWAS

Jakadun Gambia sun bukaci Jammeh ya sauka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jakadun Gambia sun bukaci Jammeh ya sauka

Gidan talbijin na kasar Gambia ya nuna shugaba Yahya Jameh ya na Allawadai da matakin da kungiyar tarayyar Afirka wato ECOWAS ta dauka na neman ya sauka daga karagar mulki bayan shan kayen da ya yi a zaben da aka gudanar a farkon watan Disamba.

Mista Jammeh dai ya sha nanata cewa an yi magudi a zaben dan haka bai amince da sakamakon ba.

Shugaba Jammeh ya ce kungiyar ECOWAS na yin katsalandan a harkokin da babu ruwanta a ciki kuma ba zai bari barazanar da su kai masa ta yi tasiri ba.

A bangare guda kuma mai magana da yawun hadakar jam'iyyun adawa da suke goyon bayan zababben shugaban kasa Adama Barrow, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa matukar Mista Jammeh ya sauka daga mulki to ba zai fuskanci shari'a ba.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi shugaban kasar da cin zarafin masu adawa da gwamnatin sa, a lokacin da ya shafe shekaru 22 yana mulkin kasar Gambia.

A baya bayan nan ne Jakadun Gambia 11 da ke aiki a kasashe daban daban sun yi kira ga shugaba Yahya Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow sannan ya yi masa murna.

Jakadun sun yi kiran ne a wani bangare na matsawa Yahya Jammeh lamba kan kalubalantar sakamakon zaben .

A wata wasika ta hadin gwiwa, jakadun sun yi kira ga shugaban na Gambia mai barin gado ya mutunta hukuncin da 'yan kasar suka yanke, sannan ya tabbatar da an mika mulki cikin kwanciyar hankali.