Nigeria: Za a biya wadanda suka tona asirin ɓarayin gwamnati

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya daura aniyar yakar cin hanci da rashawa
Gwamnatin Najeriya ta amince da wani shiri na biyan lada ga wadanda suka tona asirin ɓarayin gwamnati domin karfafa yaki da cin hanci da rashawa.
Za a bai wa wadanda suka fallasa asirin ɓarayin kashi biyar cikin dari na adadin kudaden da aka gano.
Ministar Kudi Kemi Adeosun ta ce sabon tsarin zai karfafa gwiwar 'yan kasar da suke da bayanan satar kudaden gwamnati da almundahana su fito su bayyana.
Tun bayan hawansa kan mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa, sai dai wasu na zarginsa da yi wa 'yan adawa bita-da-kulli.
Misis Adeosun ta shaida wa manema labarai a fadar gwamnatin kasar cewa, shirin zai kuma taimakawa gwamnati a yakin da ta ke yi da cin hanci da rashawa.
Sannan ta ce gwamnati ta dauki matakai domin kare jama'ar da suka bayyana bayanan daga duk wani abu da ka iya samunsu.
"Idan ka fallasa bayanai saboda Allah da kuma kishin kasa, to za a kare ka. Idan kuma kana ganin ba a kula da kai yadda ya kamata ba saboda bayanan da ka bayar, to za ka iya neman hakkinka".
Ta kara da cewa duk wanda aka ci zarfinsa sakamakon hakan, to za a biya shi diyyar duk abin da ya rasa.
Najeriya ta yi kaurin suna wurin cin hanci da rashawa, abin da wasu ke ganin shi ne ke kawowa kasar koma-bayan da ta ke fuskanta.