Za a rufe filin jirgin saman Abuja

An soki matakin rufe filin jirgin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An soki matakin rufe filin jirgin

Hukumomi a Najeriya za su rufe filin jirgin saman Abuja, babban birnin kasar domin su yi gyare-gyaren titunan jirgin.

Ma'aikatar kula da sufurin jiragen sama ta ce za a rufe filin ne tsawon makonni shida, tana mai cewa yanzu duk jiragen da ke sauka a Abuja, za su rika sauka Kaduna.

Sai dai ana fargabar sauke fasinjoji a Kaduna, musamman ganin cewa hanyar Abuja zuwa Kaduna na fama da barayin mutane domin karbar kudin-fansa.

Ma'aikatar ta kara da cewa za a rufe filin jirgin ne a watan Fabrairu, lokacin da za a fara gyaran titunan jirgin gadan-gadan.

Rufe filin jirgin zai kara dagula lissafin da fannin sufurin jiragen saman kasar ke ciki, lamarin da ke jefa matafiya cikin mawuyacin hali.

Wasu masu sharhi sun soki shirin filin jirgin, suna masu cewa matakin zai yi illa ga tattalin arzikin kasar wanda dama yake cikin matsanancin hali.