Kotu ta daure barawon gidan Rooney

Robert McNamara tsohon sojan da ya yi yunkurin satar shiga gidan Rooney

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Kotu ta daure Robert McNamara wanda ya yi kokarin satar shiga katafaren gidan Wayne Rooney

Kotu ta daure wani tsohon soja da ya yi kokarin shiga katafaren gidan Wayne Rooney, ya yi sata lokacin da dan wasan yake can yake wasan martaba shi a Old Trafford.

Robert McNamara mai shekara 24, ya amince da tuhumar da masu gabatar da kara suka yi masa a kotun Chester Crown Court.

Kararrawar fallasa barayi ce da ke katafaren gidan na fam miliyan shida da ke Prestbury a Cheshire, aka ce ta fallasa barawon a lokacin da yi yunkurin satar shiga gidan a ranar uku ga watan Agusta.

A lokacin Rooney da matarsa da 'ya'aynsu uku, Kai da Klay da Kit suna halartar wasan karramawar tsakanin Manchester United da tsohuwar kungiyarsa Everton.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Wasan na Old Trafford tsakanin kungiyoyin biyu na Rooney, an shirya shi ne domin kasancewarsa shekara 12 a Man United

Bayan kwana shida ne kuma a watan Oktoba, aka kama McNamara da ke Newby Crescent, a Scalby.

An daure tsohon sojan, wanda a kwanan nan aka gano cewa yana da 'yar larurar damuwa shekara biyu da wata takwas.

Lauyoyinsa sun sheda wa kotu cewa a farkon shekaran nan iyalansa sun nemi taimakon wata kungiya mai taimaka wa tsoffin sojoji kan larurar tabin hankali .

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

An sa gidan Wayne da Coleen Rooney a wani shirin talabijin na musamman na BBC a shekarar da ta wuce

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Wayne Rooney a dakin da yake ajiye kofunan da ya dauka