Yadda za a magance rikicin Kudancin Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai yayin da yake jawabi a fadar Sarkin Jama'a Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu

Asalin hoton, KADUNA STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai yayin da yake jawabi a fadar Sarkin Jama'a Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu

Wasu `yan asalin yankin Jama`a da ke jihar Kaduna da ake fama da rikicin ƙabilanci sun ce zai yi wuya a samu zaman lafiya a yankin matuƙar gwamnati ba ta aiwatar da shawarwarin da kwamitocin bincike daban-daban suka gabatar mata a baya ba.

Sun bayyana cewa rashin hukunta wadanda suka haddasa rigingimun da aka yi fama da su a baya ne ya sa har yanzu wasu miyagu basa shakkar ta-da-zaune tsaye a yankin.

Shugaban gidauniyar raya masarautar Jama`a, reshen Abuja, Alhaji Abdurrazak Shu`aib Muhammad a wata hira da BBC ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kafa barikin sojoji na din-din-din a yankin don magance abkuwar rikice-rikice.

Ya kara da cewa mazauna garin Kafanchan na fuskantar wahalhalu wajen gudanar da harkokin kasuwancin su sakamakon dokar takaita zirga-zirga da aka sanya a yankin a halin yanzu.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai aka tafka rikici a garin Kafanchan wanda ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Sai dai yayin wata ziyara da ya kai tare da wasu jami'an gwamnati zuwa garin Kafanchan, Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya sha alwashin magance matsalolin tsaron da ake fama da su a kudancin jahar.

Sai dai wasu mata ƙabilu na yankin da suka fusata sun gudanar da zanga-zanga tsirara a yayin da tawagar gwamnan ke ziyarar don ganin irin ta'adin da aka yi.

Masu zanga zangar sun kuma farfasa motocin tawagar gwamnan sakamakon jefe-jefe da suka riƙa yi da duwatsu duk kuwa da dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 da aka ayyana, inda suka ce sun gaji da kashe-kashen mutane da ake yi a yankin.

Tun da farko dai gwamnan Malam Nasir El-Rufai ya yiwa matan jawabi sannan ya kuma amsa tambayoyin su.