Illar shinkafar roba ga dan`adam

Shinkafar ta yi kama da wacce aka saba ci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shinkafar ta yi kama da wacce aka saba ci

Masana a harkar kiwon lafiya a Nigeria sun ce idan har ta tabbata cewa shinkafar da hukumar hana fasa ƙwauri ta kasar ta kama da roba a cikinta, to za ta iya lahani ga bil'adama.

Hukumar ta kwastam dai ta bayyana cewa ta kama buhu sama da dari na shinkafar roba da aka shigar da ita ƙasar ta harmtacciyar hanya.

Wani babban jami'in hukumar ya ce wani dan kasuwa ne ya shigar da shinkafar domin sayarwa a lokacin bukuwan kirsimeti.

Sai dai wani ƙwararren likita a asibitin Wuse da ke Abuja Dr. Salihu Ibrahim Kwaifa ya ce shinkafar robar zata iya haddasa toshewar hanjin mutum lamarin da ka iya kaiwa ga yin tiyatar gaggawa.