Za a fuskanci fari a gabashin Afrika

Manoma a yankin na matukar bukatar tallafi domin farfadowa daga masifar fari a kakar bana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manoma a yankin na matukar bukatar tallafi domin farfadowa daga masifar fari a kakar bana

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa za a samu karancin abinci a gabashin Afrika a shekara mai kamawa saboda bala'in fari da yankin ke ci gaba da fuskanta.

Tuni kimanin mutane miliyan 12 suka fara bukatar taimakon abinci bugu da kari ga karuwar 'yan gudun hijira da ake tsammanin za a samu a yankin.

Hukumar samar da abincin Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa manoma a yankin na matukar bukatar tallafi domin farfadowa daga masifar fari a kakar bana.

Shekaru biyu kenan a jere da damina bata yi kyau ba kasar Somaliya yayin da Habasha kuma ke farfadowa daga bala'in daya abkawa kasar a bara sakamakon igiyar ruwa ta El Nino.