Nigeria: An cafke ganyen wiwi na miliyoyin Naira

Hukumar kwastam ta ce zata ci gaba da sa ido don hana shigowa da duk wasu kayayyakin da aka haramta cikin kasar

Asalin hoton, NIGERIA CUSTOMS

Bayanan hoto,

Hukumar kwastam ta ce zata ci gaba da sa ido don hana shigowa da duk wasu kayayyakin da aka haramta cikin kasar

Hukumar yaki da fasa kwauri ta Nigeria da ke kula da gabar teku a Legas ta kama buhuhunan ganyen wiwi da kudinsu ya kai miliyoyin Naira.

Hukumar ta ce an shigo da ganyen wiwin ne daga kasar Ghana.

Haka kuma a wani samame na daban hukumar ta kama wani takin zamani da kudinsa ya zarta Naira biliyan biyu da bincike ya gano cewa ana iya hada bama-bamai da shi.

Shugaban hukumar mai kula da gabar teku a kudu maso yamamcin Najeriya Umar Yusuf ya ce hukumar zata ci gaba da sa ido don hana shigowa da duk wasu kayayyakin da aka haramta cikin kasar.