An ceto mutum 1,800 daga hannun Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images
Kananan yara na cikin rukunin mutanen da suka fi shan wuya saboda rikicin Boko Haram
Rundunar sojan Nijeriya ta ce ta ceto farar-hula 1,880 daga yankunan da Boko Haram ke iko da su.
Kakakin rundunar sojan Nijeriyar, Birgediya Janar, Sani Usman Kuka Sheka, ya shaida wa BBC cewa an ceto mutanen ne a cikin mako guda da ya gabata.
A cewarsa an kubutar da mutanen ne a lokacin samame a katafaren dajin nan na Sambisa, wanda ke arewa maso gabashin kasar.
Asalin hoton, Getty Images
Sojin Najeriya sun sha alwashin murkushe kungiyar
Ya kara da cewa suna ci gaba da fafutikar ganin bayan kungiyar ta Boko Haram.