Bilic: Ba inda Payet zai tafi

Slaven Bilic

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Slaven Bilic ya ce: 'Payet ya san muna son ya tsaya, kuma ya san yana da matsayi a nan'

Kocin West Ham Slaven Bilic ya ce za su yi duk abin da za su iya domin ganin gwanin sun rike babban dan wasansu Dimitri Payet a lokacin kasuwar sayar da 'yan wasa ta Janairu.

Rahotanni na nuna cewa kungioyoyi kamar su Arsenal da Manchester United na nuna sha'awarsu ta dan wasan na tawagar Faransa yayin da kasuwar ke dab da fara ci.

Bilic ya ce, ba sa son su sayar da dan wasan mai shekara 29, domin shi ne babban dan wasansu, kuma yana da kwantiragi da su, kuma mai tsawo.

A makon nan Payet ya yi hira da tashar rediyon RMC da ke Faransa, inda ya ce, zai so ya yi wasa a Arsenal karkashin Arsene Wenger, kuma ya ce yana jin takaicin rasa damar buga gasar kofin Zakarun Turai.

Sai dai Bilic ya ce wadannan kalamai ne da suka shafi dan wasan kawai., domin shi ma a lokacin yana dan wasa ya kan yi irin maganganun.