'Ana gudanar da bincike kan shinkafar roba'

Ma'aikatar lafiya ta ce babu hujjar da ta nuna cewa shinkafar da aka shigar kasar ta roba ce
Hukumomi a Najeriya sun musanta rahotannin da ke cewa an shigar da shinkafar roba kasar.
Miistan lafiya, Farfesa Isaac Adewole, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa shinkafar da aka shigar kasar ba ta roba ba ce.
A cewarsa, "Daraktan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna, NAFDAC ya yi min bayani kan rahoton shigo da shinkafar roba; amma binciken farko ya nuna cewa babu wata shaida da ke nuna hakan."
"Kanshin shinkafar daidai yake, haka ma yanayin dahuwarta da kuma launinta.NAFDAC za ta fitar da sakamakon karshe na bincikenta nan ba da dadewa ba. Kuma ina kira ga 'yan Najeriya su kwantar da hankalinsu."
Shi ma wani babban jami'in NAFDAC ya shaida wa BBC cewa suna ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da ingancin shinkafar, yana mai cewa za su yi wa 'yan kasar bayani da zarar sun kammala binciken.
A farkon makon nan ne dai hukumar hana fasa-kwauri ta Nigeria ta ce ta kama buhu 102 na wata shinkafar da aka yi da roba wacce aka shigar da ita kasar ta barauniyar-hanya.
Wani babban jami'in hukumar ya ce wani dan kasuwa ne ya shigar da shinkafar domin sayarwa a lokacin bukuwan kirsimeti.