Dan wasan Chelsea Oscar zai koma Shanghai SIPG ta China

Oscar

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Oscar ya zura wa Chelsea kwallo 38

Chelsea ta kulla yarjejeniyar sayar wa kungiyar kwallon kafar Shanghai SIPG ta China dan wasanta na tsakiya Oscar a watan Janairu lokacin da za a bude kasuwar sayen 'yan wasa.

A farkon watan nan ne dan wasan, mai shekara 25 dan kasar Brazil, ya ce an kammala "kashi casa'in cikin 100" na yarjejeniyar komawar sa Shanghai SIPG a kan £60m.

Oscar ya koma Chelsea daga Internacional a shekarar 2012 a kan £25m kuma ya zura wa kungiyar kwallo 38 a wasa 203 da ya buga mata.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce Oscar zai bar ta "a watan Janairu lokacin saye da sayar da 'yan wasa."

Oscar zai tarar da tsohon kocin Chelsea Andre Villas-Boas a Shanghai.