Dakarun gwamnatin Syria sun ce sun kwace iko da Aleppo

Bas ta karshe da ta kwashe mutane daga birinin Aleppo, da ke Syria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kwashe jama'ar da suka saura a birnin Aleppo, tare da 'yan tawaye

Sanarwar nasarar sojojin Syria, game da kwace iko da birnin Aleppo, ta fito ne daga kafafen yada labarai na hukuma, inda suka ce mota ta karshe ta kwashe raguwar mayakan tawaye da fararen hula da suka saura a birnin.

Rundunar sojin kasar ta ce yanzu ta karfafa tsaro a birnin, bayan ta kwace birnin daga hannun 'yan ta'adda.

Wannan dai uta ce nasara mafi girma da shugaban na Syria Bashar al-Assad ya samu, bayan an kwashe shekaru shidda ana yaki a kasar.

Wakili na musamman ga Majalisar Dinkin Duniya a Syria, ya ce yakamata yanzu a sake kaddamar da shirin wanzar da zaman lafiya a kasar.