Mayakan Boko Haram na ci gaba da tserewa

Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram a birnin Maiduguri

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram a birnin Maiduguri

Rundunar sojojin Nigeria ta ce mayakan Boko Haram da dama na ci gaba da tserewa daga maboyar su a dajin Sambisa sakamakon farautar su da dakarun soji ke yi a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojojin kasa ta Nigeria Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa daya aike wa manema labarai.

Sanarwar ta kuma bukaci al'umma a jihohin Adamawa da Borno da Yobe da su rika sa ido sosai tare da kai rahoto ga jami'an tsaro na duk wani mutum da ba su amince da shi ba.

Rundunar sojin ta sake jaddada cewa ta karya lagon mayakan Boko Haram kuma nan da karshen wannan shekarar dakarun sojin kasar za su kakkabe daukacin ragowar 'yan kungiyar.