Nigeria:Tasirin mayar da talabijin da radiyo kan tauraron dan`adam

Shirin mayar da daukacin gidajen talabijin da radiyo kan tauraron dan adam zai kara fadada kafofin samun labarai da musayar bayanai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shirin mayar da daukacin gidajen talabijin da radiyo kan tauraron dan adam zai kara fadada kafofin samun labarai da musayar bayanai

Masana harkokin watsa labarai a Nigeria na ci gaba da bayyana tasirin sabon shirin mayar da daukacin gidajen talabijin da radiyo kan tauraron dan adam da gwamnatin kasar ta kaddamar.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo shi ne ya kaddamar da shirin ranar alhamis a birnin Abuja.

Farfesa Osibanjo ya ce matakin zai kara fadada kafofin samun labarai da musayar bayanai a kasar.

Sau biyu dai kasar na yunkurin kaddamar da wannan aikin a baya amma abin ya faskara.

Malam Nasir Dan Ladi Bako, tsohon shugaban hukumar dake sa ido kan gidajen radiyo da talbijin na Najeriya, ya ce shirin yana da matukar alfanu sosai.

Shima a wata hira da BBC Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan shugaban gidan radiyo da talbijin na Liberty da ke jihar Kaduna a Najeriya kuma daya daga cikin masu cin gajiyar wannan sabon tsarin ya jaddada muhimmacin mayar da daukacin gidajen tallabijin da radiyo kan tauraron dan adam ga kasar.

Tun da farko kungiyar harkokin sadarwa ta duniya ta sanya watan Yuni na shekara mai kamawa ne a matsayin wa'adin da ta dibawa kasashe su mayar da gidajen radiyo da talbijin din da ke kasashen su su koma amfani da na'urori na zamani.