Birnin Aleppo ya koma karkashin ikon gwamnatin Syria

'Yan kasar Syria na murnar kwace birnin Aleppo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan kasar Syria na murnar kwace birnin Aleppo

Dakarun gwamnatin Syria sun sanar da gagarumar nasarar da suka samu, ta karbe iko da birnin Aleppo a daidai lokacin da suka ce an gama kwashe fararen hula da mayaka 'yan tawaye.

Sojojin sun ce a halin yanzu an dawo da doka da oda da kuma tsaro, a birni na biyu mafi girma a kasar Syria, bayan fafatawa da gwagwarmayar da aka dauki tsawon lokaci ana yi da 'yan tawayen da suka kira 'yan ta'adda.

Gidan talabijin din kasar ya nuna hoton bidiyon sojoji na shagulgula, tare da daga tutar kasar da kuma rera taken Syria, da furta kalaman goyon baya ga shugaba Bashar Al Assad.

Wannan nasara dai, ita ce ta farko da dakarun gwamnati suka yi tun fara yakin basasar shekaru 4 da suka wuce.

A bangare guda kuma, jakada na musamman a majalisar dinkin duniya ya ce yanzu ne lokacin da ya kamata a fara tattaunawar sulhu don kawo karshen yakin baki daya.