An samu allurar rigakafin cutar Ebola

Ebola itace annobar cuta mafi girma a tarihin kasashen yammacin Afrika

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ebola itace annobar cuta mafi girma a tarihin kasashen yammacin Afrika

An samu wata allurar rigakafi da ake saran za ta yi tasirin kashe kwayar cutar Ebola.

An dai yin gwajin allurar ne a daya daga cikin kasashen yammacin Afurka da cutar Ebola ta yi wa mummunar illa, wato kasar Guinea kasar da sai a shekarar nan aka kakkabe cutar daga ciki.

Sakamako na karshe da aka wallafa a mujallar Lancet ta Birtaniya, ya nuna dukkan mutane kusan sittin da aka yi musu allurar, bayan kwana 10 da aka sake gwada su sai aka ga babu wannan cutar a jikinsu.

Ya yin da wasu sittin da ba a yi musu riga-kafin ba, kusan ashirin da uku sun kamu da cutar.

Daraktan cibiyar bincike a Birtaniya the Wellcome Trust, ya ce samar da riga-kafin cutar Ebola abu ne da ya kamata a yaba da shi.

Fiye da mutane dubu goma sha biyu ne suka mutu a kasashen da cutar Ebola ta fi kamari a yammacin Afurka, wato Guinea, da Laberia da kuma Saliyo.