India: Mahaifi ya yi almubazzaranci a bikin 'yarsa

Amarya da Ango a bikin

Asalin hoton, JANARDHANA REDDY FAMILY

Bayanan hoto,

An yi kiyasin cewa attajirin ya kashe akalla Rupee biliyan 5, watau dala miliyan 74.

A yayin da miliyoyin al'ummar Indiya ke fama da rashin kudi, a watan Nuwambar bana ne kuma wani ya shirya wata babbar liyafa a kudancin birnin Bangalore, wanda ya sosa ran jama'a matuka.

Attajirin mai suna Gali Janardhana Reddy, hamshakin dan kasuwa ne kuma tsohon ministan kasar, ya kuma kashe makuden kudi ne wajen shirya bikin diyarsa.

Kwanaki biyar kacal bayan gwamnatin Indiya ta soke amfani da kudin 500 da 1000 a kasar watau Rupees, a wani yunkuri na dakile amfani da kudin jabu, ita dai Rumah Rasaque ta kwashe ranar Lahadi baki daya kan layin jira a gaban na'urar ciran kudi na ATM, domin ta samu ta cire Rupee 2,000- iyakar kudin da doka ta amince a cire a rana.

Rumah Rasaque dai ta shaida wa BBC cewa, a yayin tsayuwar ta a layin, babu maganar da mutane ke ta yi sai zancen bikin 'yar Mista Reddy,

Ta ce, "Duk mun ga hotunan bikin a kafofin sada zumunta, har da katin gayyatar auren, amma da yake duk gamu muna jira a layin karbar kudi, sai muke mamakin shi ina ya samu kudin wannan bushasha?"

Rumah ta kara da cewa, "A gaskia ba a yi mana adalci ba."

Asalin hoton, KASHIF MASOOD

Bayanan hoto,

Mista Reddy dai ya ce bai aikata wani laifi ba

Bikin auren dai babu musu, yana daya daka cikin bukukuwan da aka tafka almubazzaranci a kasar, inda aka yi kiyasin ya kashe akalla Rupee biliyan 5, watau dala miliyan 74.

A makonnin da suka biyo baya dai alkaluman da aka yi kiyasi sun yi kasa, amma bikin da ya dauki kwanaki biyar ana yi, ba karami bane, ganin yadda katin gayyatar ma ke da ruwan zinari a jiki, an tarbi baki dubu 50, kuma aka gayyato makada daga kasar Brazil, domin burge 'yan biki.

Mista Gali Janardhana Reddy, wanda hamshakin mai harkar ma'adanai ne, kuma tsohon Ministan ma'aikatar harkokin yawon bude ido a Indiya ne ya kashe kudin liyafar, kuma a baya ya kwashe shekara uku a gidan kaso, bisa laifin cin hanci da rashawa, kafin daga bisani aka sake shi a bara.

Mista Reddy dai ya musanata aikata ba daidai ba, kuma ya zuwa yanzu dai ba a kama shi da wani laifi ba.