'Dokar hana fita za ta sa mu yi Kirsimeti a gidajenmu'

Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai

Wasu mabiya addinin Kiristanci da ke garuruwan da dokar hana fita ta awanni 24 ta shafa da jihar Kaduna ta sanya, sun ce suna cikin halin kunci.

Kakakin kungiyar matasa ta yankin Kudancin Kaduna, Reuben Buhari, ya shaida wa BBC cewa idan dai har ba a sassauta dokar ba, to mutanen yankin ba za su yi bukukuwan kirsimeti ba.

Ya kuma ce "babu abin da dokar za ta hana idan dai har ba a magance tushen matasalar ba."

Mista Buhari ya kara da cewa " abin da kawai zai hana rikici a yankin shi ne gwamnati ta shiga daji ta kori mutanen da ke shigowa gari sun yayyanka mutane su gudu."

Sai dai kuma bangaren musulmi mazauna yankin sun ce ba sa son a cire dokar gaba daya, illa dai a dan sassauta daga shida na safe zuwa shida na yamma.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 a karamar hukumar Jama'a musamman garin Kafanchan a ranar Laraba.

Hakan ya biyo bayan wata rigima sakamakon zanga-zanga da matasa kiristoci suka yi domin nuna damuwa kan hare-haren da suka dora alhaki a kan Fulani makiyaya.

Daga baya kuma dokar ta hana fita ta fadada zuwa kananan hukumomin Zangon Kataf da Kaura.