Hana Isra'ila gini a Falasdinu ba zai yiwu ba — Netanyahu

Mista Trump ya ce abubuwa za su sauya idan ya karbi mulki a watan Janairu

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Benyamin Netanyahu ya ce zai yi tare da zababben shugaban Amurka, Donald Trump

Firaiministan Isra'ila, Benyamin Natenyahu, ya yi Alla-wadai da hukuncin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na haramta wa Isra'ila gine-gine a yankin Falasdinawa.

Da yammacin ranar Juma'a ne dai Kwamitin Sulhun na MDD ya amince da wani hukuncin, bayan kada kuri'a.

Hukuncin dai ya bayyana shirin gine-gine na Isra'ila da yi wa dokokin kasa da kasa karan tsaye.

Firaiminista Benyamin Netanyahu, a wata sanarwa, ya yi tir da wannan hukunci.

Ya kuma ce zai yi aike tare da shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump domin warware wannan hukuncin na MDD.

An dai kada kuri'ar amincewa da kudirin hukuncin ne bayan da Amurka wadda babbar kawar Isra'ilar ce, ta zama 'yar babu ruwanmu kan al'amarin.

Jakadar Amurkar a MDD, Samantha Power ta ce Amurka ba za ta yi sake da tabbatar da zaman lafiyar Isra'ila ba.

Sai dai kuma jakadiyar ta ce shawarar da kwamitin ya yanke ta yi dai-dai da tsarin Amurkar na lalubo bakin zaren zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

A baya dai Amurka ta sha yin karfa-karfa wajen danne ra'ayin sauran kasashe kan dukkan lamurran da suka shafi kasar ta Isra'ila.

To amma wannan karon ta zama 'yar baruwanmu saboda kudirin ya dace da irin ra'ayin shugaba Obama na ganin an sami dai-daito tsakanin Isra'ila da Falasdinu.