'An kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa'

Chibok schoolgirls

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana tsammanin kungiyar Boko Haram ta na tsare da wasu daga cikin 'yan matan Chibok ne a dajin Sambisa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce sojojin kasar sun fatattaki mayakan kungiyar Boko Haram daga babbar maboyarsu a dajin Sambisa.

A cikin wata sanarwa, shugaba Buhari ya ce yanzu mayakan kungiyar suna kan arcewa ne, kuma ba su da sauran wurin buya.

A 'yan makonnin da suka gabata, sojojin Najeriya sun kaddamar da babban farmaki a dajin Sambisa, dake jihar Borno.

An yi ta baza jita-jita akan cewa mayakan kungiyar Boko Haram din na rike da wasu daga cikin 'yan matan Chibok ne a cikin dajin.

Wasu daga cikin 'yan matan da suka samu kubuta bayan an sace su, sun ce an ajiye su ne a cikin dajin.

Tun daga watan Fabrairu da sojojin Najeriyar suka kaddamar da wani sabon farmaki, sojojin sun kwato yankuna da dama da a baya kungiyar Boko Haram din ke iko da su.

Shugaba Buhari ya fitar da sanarwar ce inda a ciki yake taya sojojin kasar murna game da nasarar da suka samu, wacce ya ce an dade ana tsammaninta.

Ya ce "ina so in yi amfani da wannan dama in yaba da jarunta da juriyar da dakarun rundunar Operation Lafiya Dole suka nuna, inda a karshe suka shiga, tare da cin karfin mayakan Boko Haram da suka yi saura".

Har yanzu dai mayakan kungiyar ta Boko Haram suna kai hare-haren kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya da kasashen Kamaru da Nijar masu makwaftaka.

An yi kiyasin cewa kungiyar ta halaka fiye da mutane dubu goma sha biyar, da raba wasu mutanen fiye da miliyan biyu da muhallansu a shekaru bakwai da ta shafe ta na tayar da kayar baya.