Congo: Babu yarjejeniya sai bayan Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Joseph Kabila na Jamhoriyar Dimukradiyar Condo
Shugabannin mujami'u da suke tattaunawa a Jamhoriyar Dimukradiyar Congo da nufin warware dambarwar siyasar kasar sun ce ba za a sanya hannu a wata yarjejeniyar ba har sai makon gobe.
A baya, an yi fatan cewa za a cimma yarjejeniya kan dambarwar kafin Kirsimeti.
An kashe gwamman mutane a zanga-zanga a kasar, tun da shugaba Joseph Kabila ya ki sauka daga kan mulki bayan cikar wa'adin shugabancin sa a wannan makon.
A karkashin yarjejeniyar da ake fatan cimmawa, Shugaba Kabila zai ci gaba da zama akan mulki har zuwa watan Disamban badi, sannan za a nada firayiminista daga bangaren 'yan adawa.
Sai dai duk da haka, akwai sauran takaddama game da gwamnatin gamin gambiza da za a kafa kafin a gudanar da zabe.