Dan kunar-bakin wake ya hallaka mutane a Kamaru

Cameroon attacks

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wata mata da ta jikkata lokacin wani hari a Mora a watan Janairu

Wani harin kunar bakin wake a wata kasuwa dake cike da masu sayayyar Kirsimeti a garin Mora na kasar Kamaru ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.

Wani mai taimakama gwamnan yankin Arewa mai Nisa, Midjiyawa Bakary ya ce mutanen da suka mutu sun hada da wani dalibi da kuma wata mata.

Jami'in ya ce wasu mutanen biyar sun jikkata a harin.

Ya ce dan kunar bakin waken ya yi shiga irin ta almajiri ne, yayin da ya shiga kasuwar wacce ta cika da mutane saboda Kirsimeti.

Jami'ai masu aikin sintiri sun hango shi kafin ya kaiga shiga cikin taron jama'a, amma bayan da aka tsayar da shi, sai ya tayar da bom din dake jikinsa.

A baya, 'yan kunar bakin wake da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sha kai hare-hare a garin na Mora, wanda ke nisan kilomita talatin daga iyakar Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan ikrarin gwamnatin Najeriya cewa ta fatattaki 'yan Boko Haram daga Dajin Sambisa na jihar Borno.

Kuma daman masana sun ce 'yan kungiyar za su fantsama zuwa wurare daban-daban domin kai hare-hare.