Jadawalin gasar Premier ta Ingila na ranar Litinin

Wasannin Premier na ranar Litinin
Kimanin wasanni takwas za a kara a gasar cin kofin Premier fafatawar mako na 16 a ranar Litinin. Sai a ranar Talata za a karasa saura wasanni biyu da za su rage.
Daga cikin wasannin da za a buga a gasar Premier ta Ingila ranar Litinin, Arsenal za ta kece raini da West Bromwich, Leicester City kuma da Everton
Da zarar an buga karawar a ranar Litinin, za a shiga wasannin zagaye na biyu kenan a gasar ta Premier, inda Chelsea ke mataki na daya a kan teburi, yayin da Hull City ce ta karshen teburin.