'Yan sanda sun harbe wasu 'yan bidiga a Indonesia

indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jami'an tsaron Indonesia

'Yan sanda a Indonesia sun ce sun harbe wasu mutane biyu da ake zargi 'yan bindiga masu tsananin kishin Islama ne a lardin Yammacin Java.

Wannan ne samame na baya-bayan nan da jami'an tsaro suka kai, a kokarin da suke yi na hana kai hare-hare a lokacin hutun Kirsimeti.

'Yan sandan sun ce an kashe mutanen ne a musayar wuta, lokacin da jami'an tsaro suka kai samame a birnin Purwakarta.

An kuma kama wasu mutanen biyu.

A makon jiya, 'yan sanda suka ce sun kashe wasu da ake zargi 'yan bindiga ne su uku a wajen babban birnin kasar Jakarta.

'Yan sandan kasar sun dakile yunkurin kai hare-haren bom da dama a 'yan makonnin da suka gabata, abin da ya kara haifar da zaman dardar, kan cewa masu tsatssaurar akida dake da alaka da kungiyar IS na kara karfi a kasar.