Me ya sa sana'ar saka ke neman 'gushewa'?

  • Usman Minjibir
  • BBC Hausa
Saka ta zama sana'ar tsaffi

Sana'ar saƙa na daya daga cikin sana'o'in gargajiya na Bahaushe da ya gada tun kaka da kakanni.

Sai dai kamar wasu daga cikin sana'o'in, saƙa na fuskantar barazanar ɓacewa daga ban kasa.

Da wuya dai a wannan zamani ka ga matashi yana yin wannan sana'a saboda dalilan rashin samun ribar kirki.

Garin 'Yan zaki na karamar hukumar Minjibir a jihar Kano, na daya daga cikin garuruwa da dama a arewacin Najeriya da suka shahara a wannan sana'a.

Sai dai kuma masaƙan garin wadanda mafiya yawansu dattijai ne sun koka cewa zai yi wuya sana'ar ta dore bayan ransu.

Bayanan hoto,

Dattijai sun koka cewa matasa ba sa yi watsi da sana'ar ta saka

Malam Danladi Gambo, mai shekara fiye da 60, ya kwashe fiye da shekara 55 yana sana'ar saƙa.

Amma ya ce da alama sana'ar ba za ta yi nisan kirki ba daga kansu saboda zamani da kuma rashin samun riba a sana'ar.

"Ka ga masaƙa a nan wurin ta fi guda 20 amma duba ka ga sauran nawa yanzu. Mutum shida sun mutu a nan wurin amma ba su sami magada ba."

Bayanan hoto,

Su ma tsaffin sun yi korafin cewa suna fama da rashin tallafi

Ɗanlarai 'Yan Zaki, shi ma wani masakin ne da ya gaji sana'ar kuma ya kwashe fiye da shekara 50 yana yin wannan sana'a.

Uma kamar sauran masaka, malam Ɗanlarai yana bayyana fargabar rashin samun magaji.

"Na gaji wannan sana'a daga wurin mahaifina kuma shi ma ya gada daga mahaifinsa. To amma kash! ba na jin za a samu wanda zai gaje ni saboda rashin gudanawar sana'ar."

Bayanan hoto,

Irin kayayyakin da ake sakawa take a garin 'Yan Zaki

Fargabar da wadannan tsaffi ke da ita na neman tabbata bisa la'akari da abin da wani yaro wanda ya ci kwalliya kuma yake kallon masakan ya shaida min.

Yaron mai suna Abdullahi dai ya ce ba ya fatan zama masaki saboda babu kudi a harkar.

"Direba nake son zama ba masaƙi ba domin babu kudi a sana'ar saka," in ji shi.

Shi ma Nuhu Idris wanda matashi ne ya shaida min cewa rashin samun kudi ne ya sanya shi gujewa sana'ar ta saka zuwa aikin koyarwa.

"Ya kamata ace muna yin wannan sana'a ta saka tun da gado ce amma saboda wahalar da ke ciki shi ya sa muka yi watsi da ita."

To sai dai har yanzu za a iya cewa ba a rasa yara daya zuwa biyu masu sha'awar yin sana'ar da suka gada iyaye da kakanni ba, kamar Sani Tukur.

Bayanan hoto,

Sani Tukur ya ce mutu-ka-raba tsakaninsa da saka

Sani, dan shekara 13, yana ta faman kai gwauro ya kai mari, a inda yake murza zare da kwarkwaro a cikinsa.

Ya shaida min cewa "Mahaifina ba shi da lafiya yana kwance a gida saboda haka ni ina wannan sana'ar ne domin na gaje shi."

Masakar garin na 'Yan Zaki dai ta shahara wajen saƙar rigunan saƙi da zannuwa da rawani da huluna da ma likkafani.

Bayanan hoto,

Masakan sun koa cewa ba sa samun masu gadar su

To amma kawo yanzu masu sana'ar sun ce saƙa ta zama sana'ar yin likkafani kawai domin shi ne ya fi samun kasuwa.

Sai dai kuma masakan sun ci alwashin janyo hankalin 'ya'ya da jikoki domin su yi sha'awar sana'ar amma bisa sharadin idan da za su sami tallafi.

Yanzu dai za a iya cewa masakar 'Yanv Zaki ta zama wani wuri da 'yan yawon bude ke zuwa su dauki hoto kawai.

Da kuma mutanen za su sami tallafin da suke bukata, watakila da fargabar Malam Gambo ta gushewar sana'ar, ta kau.

Bayanan hoto,

Wani dattijo ya dukufa yana saka

Bayanan hoto,

Iirin kayan da ake sakawa a Yan Zaki kenan

Bayanan hoto,

Wani dattijo a gaban injin saka, aa a cika yin sakar ba a lokacin damuna