Amurka ce kanwa-uwar gami — Netanyahu

A watan Janairu ne za a rantsar a Trump

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Donald Trump ya nemi aiki tare da Isra'ila

Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya zargi Amurka da kitsa kudirin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar na haramta mata yin gine-gine a yankin Falasdinawa.

Mista Netanyahu ya yi wannan zargin ne lokacin da ya gayyaci jakadan Amurka a kasar domin fayyace dalilin da ya sa Amurkar ta juya mata baya a wannan lokaci.

A ranar Juma'a ne dai Kwamitin Sulhun na MDD ya kada kuri'ar amincewa da kudirin da ya haramta wa Isra'ila cigaba da gine-gine a Gabar kogin Syria da Gabashin birnin Jerusalam.

Kuma Amuka ta kame bakinta daga hana kada kuri'ar kamar yadda ta saba a baya, a inda ta sha yin karfa-karfa.

Rasha da China da Burtaniya da Faransa sun goyi bayan wannan sabon kudiri.

Sharhi, Usman Minjibir

Da man dai Netanyahu ya zargi gwamnatin Barack Obama da nuna halin ko-in-kula da yanayin tsaron Isra'ila.

Hakan ne ya sa mista Netanyahu yin alwashin tafiya tare da zababben shugaban Amurkar, Donald Trump.

Mista Trump ya sha fadin cewa zai warware duk wasu matakan da aka dauka a kan Isra'ila da zarar ya hau mulki.

Donald Trump dai yana kokarin dawo da hannun agogo baya musamman ga wasu ayyuka da hukunce-hukuncen da gwamnatin Obama ta dauka.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake yi wa irin ayyukan Isra'ila kallon haramtattu ba a yankin Falasdinu.

Ko a baya-bayan nan sai da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado, Ban-Ki Moon, ya ce, Isra'ila na aikata haramci.