Ku daina karya, muna nan da ranmu - Abubakar Shekau

Abubakar Shekau

Asalin hoton, AFP

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya bayyana a wani faifan bidiyo inda ya musanta ikirarin Shugaba Muhammadu Buhari cewa sojoji sun kore su daga dajin Sambisa.

"Muna nan daranmu da lafiyarmu. Babu wanda ya kore mu daga wani wuri," in ji Shekau, wanda ya bayyana a bidiyon zagaye da wasu mayaka dauke da manyan bindigogi.

Kamfanin dillancin labarai na AFP yace a bidiyon na tsawon minti 25, Shekau ya ce "babu wanda zai iya sanin inda suke har sai idan Allah ya so hakan ya faru".

A makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya ce sojojin kasar sun fatattaki mayakan daga dandalinsu na karshe a dajin na Sambisa.

Kawo yanzu rundunar sojin kasar ba ta ce komai ba game da wannan bidiyo, wanda aka fitar a ranar Alhamis.

Abubakar Shekau ya kara da cewa: "Idan da gaske ne kun gama da mu, to ya aka yi nake magana yanzu. Sau nawa kuke yin karyar kun kashe ni?"

Ya ce "ku daina yi wa mutane karya," a wata alama ta shagube ga Shugaba Buhari wanda a makon da ya gabata ya ce sojoji sun gama da 'ya'yan kungiyar.

Babu tabbas ko a ina aka dauki faifan bidiyon, sai dai Shekau, wanda ya yi magana cikin harshen Hausa da Larabci, ya ce an nadi hoton ne a ranar bikin Kirsimeti.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Boko Haram ta fara kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2009

Wasu daga cikin abubuwan da Shekau ya fada

"Muna nan da lafiyarmu. Ba a koremu daga duk wuraren da muke zaune ba. Kuma dabarun yaki ba za su iya gano wuraren da muke ba, sai ran da Allah ya yi ikon hakan.

Bai kamata ku dunga sanar da labaran karya ga jama'a ba.

Idan har da gaske ne kun ga bayanmu, ta yaya ake gani na kamar haka? Sau nawa kuna kashe mu a kisanku na karya?

Har yanzu yakin bai kare ba, da sauransa. Fatanmu mu kafa daular Musulunci, muna kuma da daularmu ba ma cikin yankin Nigeria."

Akalla mutum 30,000 ne suka mutu a shekara bakwan da aka shafe anan rikicin na Boko Haram, yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa matsugunansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kimanin mutum 100,000, yawancinsu yara kanana, ka iya mutuwa saboda yunwa idan ba a dauki matakan gaggawa ba.