Rasha: An tsamo gawarwaki 10 da suka mutu a hadarin jirgi

Masu aikin ceton Rasha a tekun Bahar Maliya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Har yanzu masu aikin ceto na cigaba da aiki a tekun Bahar Maliya

Rasha ta ce an samo gawarwaki goma cikin mutanen da hatsarin jirgin saman kasar ya rutsa da su a tekun Bahar Maliya, an kuma mayar da su birnin Moscow.

Dukkanin fasinjoji 92 da ma'aikatan jirgin yakin sun mutu, bayan da ya fado jim kadan da tashinsa daga birnin Sochi.

Jirgin dai yana kan hanyarsa ta zuwa yankin Latakia ne na kasar Syria.

Cikin wadanda suka mutu har da fitattun 'yan tawagar sojin Rasha da ake cewa Alexandrov.

Minsitan sufurin Rasha, Maxim Sokolov, ya ce ana tunanin matsalar na'urar da jirgin ya samu ce ta yi sanadin hatsarin.

Ana cigaba da gudanar da gagarumin aiki tare da masu aikin ceto 3,000, domin binciko sauran mutanen da lamarin ya shafa.

Jirgin ya taso daga birnin Moscow sannan ya sauka a filin jirgin saman Adler da ke Sochi domin ya kara mai.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron ta Rasha ta fitar ta ce, "An gano wasu sassan jirgin samfurin Tu-154 a nisan kilomita da rabi daga tekun Bahar Maliya da ke kuryar Sochi."