Gwamnatin Nigeria ta gano ma'aikatan boge 50,000

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa

Gwamnatin Najeriya ta ce ta gano ma'aikatan boge kimanin 50,000 da ke karbar albashi a duk wata.

Ta kara da cewa hakan ya sa ta samu rarar Naira Biliyan 200 a wannan shekarar ta 2016 da ke karewa.

Daya daga cikin masu magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da manema labarai.

Malam Garba ya ce an kuma kama mutane 11 da suka kware wajen cuwa-cuwar karbar albashin da sunan ma'aikatan boge, kuma an mika su ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC.

Ya ce a duk wata gwamnati na adana Naira biliyan 13 daga albashi, da kuma Naira biliyan daya da miliyan 500 daga kudin fansho.

Mai taimakawa shugaban ya ce a yanzu gwamnati na biyan Naira biliyan 138 a duk wata a matsayin albashi, maimakon Naira biliyan 151 da ake biya a baya.

Sannan kuma kudin da ake biya na fansho a baya ya kai Naira biliyan 15 da rabi amma yanzu ya komo Naira biliyan 14 da doriya.

Tun bayan hawansa mulki, Shugaba Buhari ya ce ya dauki wasu matakai domin dakile cin hanci da rashawa, wanda ya yi wa kasar katutu.