'Yan Boko Haram 31 sun mika wuya a Niger'

Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tun a watan Junairun bara ne 'yan Boko Haram ke kaddamar da munanan hare-hare a jamhuriyar Nijar

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce mayakan kungiyar Boko Haram 31 sun zubda makamansu tare da mika wuya ga gwamnatin kasar.

Ministan cikin gida Bazoum Muhammad ne ya sanar da hakan a ranar Talata a shafinsa na Twitter, kuma wannan ne karo na farko da kasar ke sanar da mika wuyan da 'yan Boko Haram din suka yi.

Wani jami'in tsaro a yankin Diffa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa daya bayan daya suka dinga mika wuya a lokuta mabanbanta kuma a yanzu haka an killace su a wani wuri tare da ba su cikakken tsaro.

Tun a watan Fabrairun shekarar 2015 'yan Boko Haram suka fara kaddamar da munanan hare-hare da kisan mutane a jamhuriyar Nijar.

A farkon bara ne wani babban jami'in tsaroa a yankin Diffa ya sanar da cewa matasa na kara shiga kungiyar ta Boko Haram, saboda kudin da take kwadaitar da su na albashi da ya kai dala 520 kwatankwacin Naira 260,000 a kowanne wata.

Kawancen kasashen Najeriya, Nijar, da Chadi sun kaddamar da yunkurin fatattakar 'yan Boko Haram daga yankunan su a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Harwayau, a watan Oktobar da ya wuce, gwamnatin Nijar ta sanar da irin nasarar da ta ke samu a yakin da ta ke yi da 'yan kungiyar.

Yayin da a bangare guda su ma hukumomin Najeriya ke sanar da dakile ayyukan da mayakan kungiyar ke yi a kasar.