Wani mutumi ya mutu a bikin ranar haihuwar wata yarinya

Asalin hoton, EPA
An gudanar da liyafar Rubi Ibarra Garcia ne a waje, inda aka yi addu'o'i domin karrama ta a ranar
Wani mutum ya rasa ransa yayin bikin zagayowar shekarar wata yarinya, mai suna Rubi Ibarra Garcia, a Mexico, bayan da iyayenta suka mika gayyata ga dubban mutane a shafin sada zumuta.
Mutumin ya rasu ne bayan da ya keta gaban wani doki da ke gudu a yayin gasar tseren dawakai da aka shirya wa yarinyar da ta cika shekaru 15.
Kafafan yada labaran kasar sun ce daya daga cikin dawakan da ke gasar ta masu koyo, na marigayin ne, wanda ke da shekaru 66.
Akalla mutane miliyan 1.3 ne suka yi alkawarin halartar bikin, wanda aka gayyaci makada kuma aka yi rabon abinci.
A wata sanarwa ta faifen bidiyo, mahaifin Rubi, Crescencio Ibarra, ya shaida wa al'ummar yankin su na La Joya cewa, zai shirya wa diyarsa babbar liyafa domin murnar cikarta shekara 15.
Ya kuma kara da cewa za a yi gasar tseren dawaki, kuma duk wanda dokinsa ya yi nasara za a bashi kudin kasar Pesos 10,000, kwatankwacin dalar Amurka 490.
Mista Felix Pena, wani mai kiwon dawaki a gonar sa ta Coyotes Negros, na daya daga cikin wadanda gasar ta janyo wa hankali.
Mista Pena ya shaida wata kafar labaran yankin Hora Zero, cewa zai shigar da dokinsa Oso Dormindo gasar.
Ya ce, "Ba zan shiga gasar ne domin kudin ba kawai, amma domin daukakar da zan samu idan dokin ya yi nasara."
A wani bidiyo dai da ya nuno yadda wasan ya kaya, an hango yadda Mista Pena ya shiga filin tseren, inda dawakan suka rinka tattake shi cikin kura.
Asalin hoton, AP
Dubban mutane ne suka halarci bikin na Rubi
Ba a dai tabbatar da dalilin da ya sa Mista Pena, wanda ke yawan harkar tseren dawakai ya shiga filin ba.
Wasu da ke filin dai sun ce akwai yiwuwar ya yi kuskure wajen duba nisan cikin filin ne, a yayin yaba wa dokin nasa.
'Yan sanda dai sun ce baya ga wannan hatsarin da ya afku, an yi bikin lafiya.