An gano na'urar nadar bayanai a Jirgin Rasha da ya fadi

Wasu da ke mika alhinin su ga mamatan wajen sanya furanye

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Iyalan wadanda suka rasu cikin jirgin, na zaman makoki

Masu bincike a Rasha, sun samu daya daga cikin na'urorin nadar bayanan taswirar tafiyar jirgin saman sojin nan da ya fadi a tekun Bahar Maliya, a ranar Lahadi, wanda ya yi sanadin mutuwar dukkan mutane 92 dake ciki.

An samu na'urar kimanin nisan kilomita 1600 daga gabar teku, kuma an kai ta birnin Moscow domin nazari.

Mai magana da yawun Rundunar sojan Rasha ya ce na'urar nadar bayanan, wadda ake kira 'Black Box' a turance, ta na cikin yanayi mai gamsarwa, ana kuma fatan za ta samar da muhimman bayanan musabbabin faduwar jirgin, jim kadan bayan tashinsa daga Sochi.

Masu aikin ceto sun kuma gano daya daga cikin injinunan jirgin.

Ana dai ta hasashe game da ainihin dalilin hadarin jirgin, inda ake zaton tangardar na'ura ce ko kuma fashewar wani abu a cikin jirgin yayin da yake kan hanyarsa ta tafiya.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da laluben gawarwakin mutanen da hadarin ya rutsa da su a cikin teku.