Carrie Fisher ta 'Star Wars' ta mutu sanadiyyar bugun zuciya

Harrison Ford da Carrie Fisher a fim din Satr Wars

Asalin hoton, 20TH CENTURY FOX VIA AP

Bayanan hoto,

Carrie Fisher ta zamo fitacciyar 'yar fim ne bayan nasarar jerin fina-finan Star Wars

Carrie Fisher, dai ta yi suna bayan da ta fita a matsayin Princess Leia, watau Gimbiya Leia a fitaccen fim din nan na Star Wars.

'Yar fim din ta rasu tana da shekaru 60.

Abokan tafiyar ta cikin jirgin da ya taso daga California zuwa Landan, sun ce ta samu matsalar numfashi na tsawon mintuna, kuma bayan nan ta kwanta a sashen kula na gaggawa a wani asibiti da ke jihar Los Angels.

Wani mai magana da yawun iyalanta Billy Lourd, ya tabbatar da cewa ta mutu ne 'yan mintuna kafin karfe 9 a safiyar ranar Talata.

An haifi Carrie Fisher a cikin iyalan da ke harkar fina-finai, inda mahaifinta Eddie Fisher, mawaki ne ita kuma mahaifiyar ta Debbie Reynolds kuma fitacciyar 'yar fim ce.

A baya ta tabbatar da famar da ta ke ta yi da yawan shan barasa da kwayoyi, a wani littafi da aka wallafi kan labarin ta mai suna, 'wishful Drinking.'