Japan ta nemi gafarar Amurka

Mr Abe da shugaba Barrack Obama sun ajiye furanni a wani bikin addu'o'i

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mr Abe da shugaba Barrack Obama sun ajiye furanni a wani bikin addu'o'i

Firai ministan kasar Japan, Shinzo Abe, ya ziyarci sansanin sojin ruwa na Amurka dake Pearl Harbor inda ya mika ta'aziyya tare da neman gafara ga iyalan mutanen da suka mutu a harin da Japan ta kai kimanin shekaru 75 da suka gabata.

Mr Abe ya yi jawabi ne tare da shugaba Barrack Obama bayan da shugabannin biyu suka yi ajiye furanni a wani bikin addu'o'i da aka shirye a wajen da jirgin ruwan Amurkar ya nutse.

Shugaba Obama ya ce ziyarar Mr Abe wata manuniya ce cewa duk da rarrabuwar kai da yaki ya haddasa, za'a iya ci gaba da kulla kyakyawar dangantaka da zata samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Wakiliyar BBC ta ce sai dai wannan wani yanayi na rashin tabbas game da dangantaka tsakanin Amurka da Japan a daidai lokacin Mr Obama ke shirin mika mulki ga Donald Trump wanda ya ce zai soke kawancen da aka kulla ta kasuwanci tsakanin kasashen biyu.