Tilas a yi gwajin cutar HIV kafin aure a Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar

Asalin hoton, JIGAWA STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar

Gwamnatin jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya ta rattaba hanun kan wata doka da ta wajabta yin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki ga duk mutanen da suke shirin yin aure a jihar.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin rage yaduwar cutar ta HIV a jihar bayan gano cewa ana saurin yada cutar tsakanin ma'aurata.

Mataimakin gwamnan jihar Barister Ibrahim Hassan Hadejia ya shaidawa BBC cewa an samar da wuraren yin gwajin kyauta a sassa dabam dabam na jihar.

Dokar ta tanadi hukunci ga duk wanda ya nuna kyamata wajen yin gwajin kafin yin aure da kuma hana tsangama ga wadanda aka samu suna dauke da cutar.