India: An kama masu safarar macizai masu dafi

Macizai masu dafi 70 da aka killace

Asalin hoton, PRATIBHA WALUNJ

Bayanan hoto,

Mutanen sun ce suna kiwon macizan ne domin tatsar dafin su

'Yan sanda a birnin Pune dake yammacin India sun kama mutane biyu bayan da aka samu macizai fiye da saba'in masu mugun dafi a wani gidan haya.

An samu kububuwa fiye da arba'in da kuma gamasheka talatin a cikin akwatuna da buhuhuna a wani daki, wanda rahotanni ke cewa a cikinsa wani mutum da matarsa da 'ya'yansu ke kwana tare da macizan.

'Yansanda sun ce mutanen da aka kama, sun sayi macizan ne daga masu wasa da maciji, ko kuma sun kama su ne a daji, domin tatsar dafinsu.

Masu sayar da dafin maciji dai na cabawa a wasu sassa a kasar India, amma killace namun daji haramun ne a kasar.