John Kerry ya gargadi Isra'ila kan Palasdinu

Kayan gine-gine da suka soma aiki

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Isra'ila dai ta dage da cewa sai ta gina wa al'ummarta gidaje a yankin Palasdinawa

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya ce yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tsakanin kasashen Isra'ila da Palasdinu na fuskantar barazana.

John Kerry dai ya nanata cewa haramta wa Isra'ila gini a yankin Palasdinu da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, ya zo daidai da akidar Amurka.

Da farko dai shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ta shafinsa na Twitter ya ce haramcin da aka yi wa Isra'ila bai dace ba, kuma a cewarsa, ba zai bari a yi wa Isra'ila cin fuska ba.

Wani kwamitin karamar hukuma a Birnin-Kudus, ya dakatar da shirin kada kuri'a game da gina karin sabbin gidaje 500 ga 'yan Isra'ila a gabashin birnin,

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a dakatar da gina matsugunan Yahudawa a yankin Palasdinawa da Isra'ila ta mamaye.

Wani da ke cikin kwamitin ya shaida wa BBC cewa ofishin Firayi Minista ne ya bukaci a dauki matakin, domin kauce wa kara sukurkucewar hulda da Amurka, gabanin wani jawabi da sakataren harkokin wajen Amurkar, John Kerry, zai yi game da shirin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya wanda ya ci tura.

To sai dai babban mai shiga tsakani na Palasdinawa, Saeb Erekat, ya ce kamata ya yi Firayim-Minsitan Isra'ila ya dakatar da shirin na gina matsugunan baki daya.

Mista Erekat ya ce, Mista Netanyahu yana sane da cewa yana da zabi, ko dai gina matsugunan ko kuma zaman lafiya, ba zai iya samun duka biyun ba.

Ya kara da cewa, gina gidajen yin karan-tsaye ne ga dokokin duniya.