'Mun cafke 'yan Boko Haram 1,240'

Dakarun Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ce rundunar sojin Najeriya ta kama wasu da ake zargi 'yan Boko Haram ne su 1,240, a yayin wani samame da dakaru suka kai a dajin Sambisa.

Manjo-Janar Lucky Irabor, wanda ke jagorantar aikin tsaro na Operation Lafiya Dole, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a wani sansanin soji da ke Maiduguri.

Irabor ya ce mutum 413 daga cikin wadanda ake zargin maza ne manya, sannan 323 manyan mata ne, sai yara maza 251 da kuma yara mata 253.

Ya ce, "Muna yi masu tambayoyi, domin mu tabbatar ko 'yan Boko Haram ne, saboda mun san babu yadda za a yi wani da baya cikin kungiyar Boko Haram, ya zamana yana cikin dajin na Sambisa."