Shugaba Koroma ya ba da wa'adin sasanta rikicin kwallon kafar Sierra Leone

Shugaba Koroma na Sierra Leone

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Koroma ya yi gargadi cewa ba wanda zai samu kariyar Fifa

Shugaba Ernest Bai Koroma na Saliyo ya umarci manyan jami'an kwallon kafa na kasar wa'adin zuwa watan Maris na 2017da su sasanta tsakaninsu.

Shugaban ya tsoma baki ne a kan rikicin, wata daya kawai bayan babbar sakatariyar hukumar kwallon kafa ta duniya Fatma Samoura ta ziyarci Freetown, inda ta bayyana wani tsari na sasanta rikicin da ake yi tsakanin manyan jami'an kwallon kafar kasar.

Shugabar hukumar kwallon kafa ta Saliyon (SLFA) Isha Johansen na rikici ne da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa, musamman a kan sauye-sauyen da take kawowa da kuma kiran babban taron hukumar.

Hukumar kwallon kafar ta kuma kasa shirya gasar lig ta kasar a bana, amma wasu kungiyoyi tara daga cikin 14 na kasar a yanzu suna gudanar da gasar lig da suka shirya da kansu.

Shugaba Koroma wanda sau da dama ya yi kokarin kawo karshen rikicin da ke shafar kwallon kafar kasar tasa, bai bayyana matakin da zai dauka ba idan ba a kawo karshen rikicin ba bayan wa'adin.