Boksin: 'Na yi ta kokarin kashe kaina'

Ricky Hatton a lokacin da ya yi nasara
Bayanan hoto,

Ricky Hatton ya ce: ''Daga shan barasa ne sai na mike zuwa shan miyagun kwayoyi, ba kakkautawa''

Tsohon zakaran damben boksin na duniya ajin marassa nauyi Ricky Hatton ya ce sau da dama ya yi kokarin kashe kansa a faman da yake yi da larurar damuwa.

Dan Birtaniyar mai shekara 38, wanda ya yi ritaya daga dambe a 2012 ya ce: ''Na kan je gidan giya, na dawo, na dauki wuka na zauna a cikin duhu ina ta rusa kuka.''

Hatton dan Manchester, wanda ya taba hira da BBC a 2011 a kan yunkurin kashe kansa da kuma damuwa da yake fama da ita a lokacin, ya ci kambin duniya na ajin marassa nauyi da kuma na matsakaita nauyi.

Tsohon zakaran na duniya kuma bayyana bukatar bullo da wani tsari na taimaka wa 'yan damben boksin da suka yi ritaya, wadanda suke da larurar damuwa.

An karbe lasisin yin dambe na Hatton a 2010 bayan da ya yarda cewa yana amfani da hodar iblis ta koken.

Hatton wanda ya yi ritaya shekara daya bayan nan, a 2011, kafin ya sake dambe sau daya, yanzu mai mai horar da 'yan damben boksin ne da kuma hada damben.