Sojojin Najeriya sun karyata Abubakar Shekau

Sojojin Najeriya sun ce Shekau baya Sambisa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojoji sun karyata Shekau

Rundunar sojan Najeriya ta musanta ikirarin da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi a wani faifan bidiyo da kungiyar ta fitar, inda ya musanta cewa sojojin Najeriya sun kore su daga maboyarsu da ke dajin Sambisa.

Rundunar sojin ta ce idan har da gaske 'ya'yan kungiyar na cikin dajin to su fadi a inda suke kasancewar akwai sojoji a cikin dajin.

Rundunar ta bakin kakakin shalkwatar tsaro ta Najeriya, Birgediya Janar Rabe Abubakar ta ce wannan bidiyo da kungiyar ta fitar wanda aka nuna shugabanta Abubakar Shekau, shure-shure ne wanda baya hana mutuwa.

Birgediya Janar Rabe Abubakar ya ce sojojin su sun yi rawar gani wajen fatattakar 'ya'yan kungiyar daga dajin, tare da kubutar da mutane da dama, dan haka ba dai 'ya'yan kungiyar a dajin Sambisa ba, sai dai wani dajin.

Haka kuma a wata sanarwa kakakin rundunar sojojin kasa ta Nigeria Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar ta ce Boko Haram tana son kawai ta sanya tsoro ne a zukatan mutane, amma duka sansanonin Boko Haram a yanzu suna hannun sojoji.

A cikin bidiyon dai Shekau ya ce "babu wanda zai iya sanin inda muke har sai idan Allah ya so hakan ya faru".

A makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya ce sojojin kasar sun fatattaki mayakan daga sansaninsu na karshe a dajin na Sambisa.

Akalla mutum 30,000 ne suka mutu a shekara bakwan da aka shafe anan rikicin na Boko Haram, yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa matsugunansu.