An kafa rundunar tsaro ta musamman a Kudancin Kaduna

Rundunar Operation Harmony ta cafke wasu matasa dauke da makamai da albarusai a kudancin jahar Kaduna
Bayanan hoto,

Rundunar Operation Harmony ta cafke wasu matasa dauke da makamai da albarusai a kudancin jahar Kaduna

A Najeriya, hukumar 'yan sanda ta kafa wata runduna ta musamman domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kudancin jahar Kaduna.

An samu tashe tashen hankula ne bayan wata zanga zangar lumana da ta rikide zuwa rikicin addini da kabilanci.

Rundunar mai suna Operation Harmony ta ce da fara aikinta, ta cafke wasu matasa sama da goma dauke da makamai da albarusai a kudancin jahar ta Kaduna.

Sai dai duk dai matakan da rundunar ke cewa ta na dauka na dawo da zaman lafiya a yankin da kuma dokar hana fita, har yanzu rahotanni na nuna cewa ana samun karin arangama wacce ke haifar da asarar rayuka.