Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Syria

Yarjejeniyar ta biyo bayan nasarar kwace Aleppo da sojojin Syria suka yi daga hannun 'yan tawaye

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Yarjejeniyar ta biyo bayan nasarar kwace Aleppo da sojojin Syria suka yi daga hannun 'yan tawaye

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta kasa baki daya da aka cimma tsakanin gwamnati da bangarorin 'yan tawaye ta fara aiki a Syria.

An dakatar da artabu a fadin kasar, sai dai wasu rahotanni sun ce an yi ta bata kashi a wasu wurare.

Yarjejeniyar ce matakin da aka dauka a baya bayan nan don kawo karshen yakin ba-sa-sa a Syriar da aka kwashe shekaru shida ana yi, kuma kasashe kamar Rasha da Turkiyya da Iran ne ke goyon baya wannan yunkuri.

Amurka dai ba ta ciki, yayin da sauran bangarorin suka nuna aniyarsu ta fara tattaunawar sulhu.