Babu kakkyawar tsarin kiwon lafiya a duniya- Bill Gates

Mr Gates ya ce annobar Ebola da ZIKA sun nuna cewa duniya bata da kakkyawar kariya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mr Gates ya ce annobar Ebola da ZIKA sun nuna cewa duniya bata da kakkyawar kariya.

Fitaccen attajirin nan Bill Gates ya yi gargadin cewa yadda tsarin kiwon lafiya na duniya yake a halin yanzu, ba zai iya shawo kan barkewar cuta mai hadari ba kamar mura.

A wata hira da BBC Mr Gates ya ce annobar cututtuka kamar Ebola da ZIKA da suka bulla sun nuna cewa duniya bata da wata kakkyawar kariya.

Ya kara cewa wadanan cututtukan sun kara fitowa fili da irin raunin kasashen duniya wajen iya kirkiro da sabbin magunguna da kuma alluran rigakafi cikin gaggawa.

Wakilin BBC ya ce cikin shekaru 16 da suka gabata, Gidauniyar Bill and Melinda Gates ta kashe biliyoyin daloli wajen samar da allurar rigakafi ga kasashen duniya matalauta.